A yayin da ya rage kwanaki biyu a kammala ayyukan rajistar mutanen da suka cancanci samun katin zabe a rukunin farko da ya kumshi jihohi 4, shugabannin hukumar zaben Jamhuriyar Nijar sun bayyana gamsuwa da yadda wadannan ayyukan ke gudana.
A yayin taron da ya kira a wannan juma’a domin sanar da shugabanni da wakilan jam’iyun siyasa halin da ake ciki dangane da ayyukan rajistar da aka fara a ranar 15 ga watan Oktoban 2019 a jihohin Agadez, Tahoua, Tilabery da Dosso, shugaban hukumar zabe ta kasa (CENI) Issaka Souna ya ce duk da kalubalen da aka fuskanta a ranakun farkon soma wannan aiki abubuwa na tafiya kamar yadda aka tsara.
A ranar 19 ga watan nan na Janairu ne ya kamata a kammala ayyukan rajista a wadannan jihohi 4 inji shugaban hukumar zabe.
Kuma a cewarsa, ya zuwa yanzu mutum 623,765 ne aka yi wa rajista ya zuw ayanzu.
Sai dai shugaban jam’iyyar MPA Bunkasa, Mahaman Sidi Abdoullahi na gungun jam’iyu ‘yan baruwanmu dake daya daga cikin mahalarta wannan taro ya nuna damuwasa a game da wadanan alkaluma..
Anan gaba kadan ne za a fara irin wadannan ayyukan rajista a jihohin Zinder, Maradi, Diffa da Yamai kamar yadda abin zai shafi ‘yan Nijar mazauna kasashen waje don ganin an hada kundin rajistar.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Jamhuriyar Nijar.
Your browser doesn’t support HTML5