Nijar: Bangarorin Jam'iyyar CDS Rahama Sun Yi Sulhu

Yanzu haka bangarori biyu da basa jituwa a jam'iyyar CDS Rahama a Jamhuriyar Nijar sun rattaba hannu akan wata yarjejeniya ta hadewa wuri guda, domin yin aiki tare.

A Jamhuriyar Nijar bangarorin da ke rikicin shugabanci a jam’iyyar CDS Rahama sun cimma yarjejeniya da nufin kawo karshen hamayyar da ke tsakaninsu da nufin tunkarar zabubukan 2020 da 2021, saboda haka aka mika ragamar shugabanci a hannun daya daga cikin dattawan jam’iyyar domin rikon kwarya.

Kakakin jam’iyyar CDS Rahama, Moutari Kadri, shine ya karanto sanarwar hadin gwiwar bangarorin da ke hamayyar shugabanci bayan shafe watanni ana tuntubar masu bakin fada aji a wannan jam’iyya da ta tsinci kanta cikin halin wargajewa.

Alhaji Abdou Amani shine ke shugabancin dayan bangaren da su ka amincewa wannan sabuwar tafiya.

Shi ma jagoran bangare na biyu na wannan jam’iyya, Boubacar Madougou, ya amince da wannan mataki sai dai ya gargadi abokan tafiya akan batun mutunta ka’idodin jam’iya don cimma gurin da aka sa gaba.

‘Ya’yan jam’iyyar CDS Rahama wadanda su ka halarci wannan buki na dinke baraka na ganin abin a matsayin wani ci gaban demokradiyya.

Bangarorin biyu sun damka komai na shugabanci a hannun daya daga cikin dattawan jam’iyar, domin jagorancin tsare tsaren taron “Congress” na kasa da ake sa ran gudanarwa a ranar 21 ga watan nan na satumba.

Jam’iyyar CDS Rahama ta dora shugabanta, Mahaman Ousman, akan kujerar shugancin kasa a zaben 1992 kafin Abdou Labo ya karbe ragamar jam’iyyar a kotu koda yake a baya bayan nan wani hukuncin kotu ya haramta masa shiga hakokin siyasa.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Nijar- Bangarorin Jam'iyyar CDS Rahama Sun Hade Guri Guda