Jamhuriyar Niger ta Kebe Kowane 30 ga Watan Nuwamba Ranar Girmama 'Yanjarida

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Majalisar Ministocin Jamhuriyar Niger ta amince da kebe ranar 30 ga kowane watan Nuwamba duk shekara ta zama ranar karrama da girmama 'yanjarida.
A yayin wani taron ministoci gwamnatin jamhuriyar Niger ta aminta da kebe ranar kowane 30 ga watan Nuwamban kowace shekara ta zama ranar 'yancin 'yanjarida da kuma girmamasu.

Ranar zata zama ranar kyautata fadan albarkacin baki da karrama 'yanjarida. Ranar ta zo daidai da ranar da shugaban kasa Mohamadou Issoufou ya sanya hannu ga wata takarda inda yace a cikin mulkinsa ba za'a kama ba ko kuma kargame danjarida ba ko kuma tasa kyeyarsa zuwa gidan kurkuku ba. Ya yi wannan sa hannun ne a shekarar 2011. To amma kawo yanzu nan aka tsaya domin ba'a aiwatar da kudurin ba.

Mallam Bello Bubakar shugaban 'yanjaridar Niger yace sun so a dauki wannan mataki fiye da shekara daya da ta wuce lokacin da suka bayar da shawara amma a wancan lokacin ba'a sauraresu ba. Yace sai yanzu da abun ya lalace. A cewarsa an makara da daukan wannan matakin.

A cewar Bubakar Jello duk wata barnar da ake yi jamhuriya ta bakwai ta riga ta yisu. Ta dauki wasu matakai da suka rugurguza hukuma domin cikin wata daya wannan shekarar 'yanjarida tara ne aka tasa kyeyarsu zuwa cikin kurkuku har da wakilin Muryar Amurka. Wuraren dake neman gyara tun lokacin ya kamata a yi ba yanzu ba da abubuwa sun riga sun lalace. Kakakin gwamnati ya fito ya karanta laifukan da yace 'yanjarida sun yi kuma wanshekare aka cafke 'yanjarida tara. Laifin shugaban kasa ne da gwamnatinsa domin ya gaza wurin tabbatar cewa an yi aiki da kudurin.

Ga cikakken bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Niger ta Kebe 30 ga Kowane Watan Nuwamba Ranar Girmama 'Yanjarida - 3'00"