Jam’iyyun Adawa Biyu Sun Goyi Bayan Jam’iyyar PNDS a Jamhuriyar Nijar

Zaben Nijer

Zaben Nijer

Jam’iyyun da suka zo na uku da hudu a zagayen farko na babban zaben shugaban kasa a jamhuriyar Nijar, sun bada sanarwar hada kai tare da mara wa dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki baya.

An gudanar da zagayen farko na babban zaben shugaban kasa a jamhuriyar Nijar tun ranar 27 ga watan Disamban bara, inda dan takarar jam’iyyar MNSD NASARA ya zo na uku. Sai kuma dan takarar jam’iyyar MPR Jamhuriya wanda ya zo na hudu.

Baki daya jam’iyyun adawar biyu MNSD da MPR sun jaddda goyon bayansu ga dan takarar jam’iyyar PNDS mai mulki Bazoum Mohamed, wanda zai kara da dan takarar jam’iyyar RDR Alhaji Mahaman Ousman, a zaben zagaye na biyu da za a gudanar ranar 21 ga wannan wata na Fabarairu.

A zagayen farko na zaben 27 ga watan Disamban 2020, Bazoum Mohamed ya sami kashi 39.30 na kuri’un da aka kada, saboda haka samun goyon baya daga Seini Oumarou mai kashi 8 da Albade Abouba mai kashi 7, wani abu ne da ke saka walwala a zukatan magoya bayan jam’iyar PNDS Tarayya, wadanda ke ganin za su iya lashe zaben.Yayin da magoya bayan dan takarar RDR Canji, Mahaman Ousman ke cewa ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam’iyyun Adawa Biyu Sun Goyi Bayan Jam’iyyar PNDS a Jamhuriyar Nijar - 2'38"