Sun kuma bayyana iri-irin matakan da za su dauka a fannin ilimi, farfado da komadar tattalin arziki, samar da tsaro, da kuma samar da shugabanci nagari.
Masu ruwa da tsakin daga karkashin inuwar jam’iyyun siyasa daban-daban kamar su PDP, ADC, PRP, Boot party da dai sauransu sun bayyana irin ababen da za su sanya a gaba idan Allah ya ba su nasara a zaben na wata Febrairun ne, a yayin taron da ofishin Majalisar dinkin duniya a Najeriya ya shirya don ji daga bakin dukkan wadanda suka halarci taron, a game da matakan da za su dauka don tabbatar da an cimma kudurorin nan 17 na raya kasashe wato SDGs idan aka kafa sabuwar gwamnati.
A yayin taron, an tattauna muhimman abubuwa kama daga irin dabarun da za’a yi amfani da su wajen farfado da bangaren ilimi, tattalin arziki, magance matsalolin tsaro, komawa asalin tsarin tarayya, da kuma samar da shugabanci nagari don tafiya da dukkan ‘yan kasa ta yadda ba wanda zai rinka ganin ana zalintar shi.
A jawabinsa yayin taron, babban jami’in majalisar dinkin duniya a Najeriya, Matthias Schmale, ya bayyana gamsuwarsa da yadda dukkan jam’iyyun da suka amsa gayyatar ofishinsa suka mayar da hankali a kan samar da mafita ga matsalolin da ake fama da su a kasar, a maimakon zagi ko cin mutuncin juna, yana mai cewa ya ji dadin yadda dukkan jam’iyyun suka fayyace inda zasu ba da karfi idan aka kafa sabuwar gwamnati.
Kwamared Muhammad Bello Ishaq, mataimakin kakakin jam’iyyar PRP na kasa wanda ke cikin mahalarta taron ya ce jam’iyyarsu ta ginu a kan girmamawa ko daidaito na dan adam da sauran muhimman ayyuka, ya kara da cewa abin da ya jawo rashin tsaro shi ne lalacewar shugabanci, kuma a shirye jam’iyyar PRP take ta samar da shugabanci nagari.
Jam’iyyar PDP ta sami wakilcin, Mrs Agape Kremer, shugabar sashen kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje na kwamitin yakin neman zaben jam'iyar, ta bayyana cewa idan suka sami nasara dan takararsu, Atiku Abubakar, zai fara ne da tattara sahihan bayanai a game da yanayin da makarantun kasar ke ciki don daukan matakai da za su inganta fannin don amfanin ‘yan kasa baki daya.
A hirar shi da Muryar Amurka Alhaji Sa’id Baba Abdullahi babban sakataren jam’iyyar ADC a matakin kasa, ya ce za su ba da fifiko ga bangaren ilimi idan suka kafa gwamnati, domin duk abun da ba’a yi da ilimi ba, ana samun akasi.
A ranar 25 ga watan Febrairu ne, Najeriya, kasar dake tafiya a tsarin mulkin dimokuradiyya mafi girma a nahiyar Afirka za ta gudanar da babban zabenta na bakwai tun bayan komawar mulkin farar hula a shekarar 1999.
Za a gudanar da zaben a Najeriya ne watanni kadan kafin kasar ta cika shekaru 30 da soke zaben shugaban kasa na shekarar 1993, wanda ake yi wa kallon “mafi inganci cike da amfani da ‘yancin yan kasa da walwala kuma mafi adalci a tarihin kasar.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5