Jam'iyyar Adawa A Jam'huriyar Kamaru Na Ci Gaba Da Fafutukar Neman Sauya Gwamnati

Jagoran ‘yan adawar kasar jamhuriyar Kamaru, Ni John Fru Ndi, Jagoran ‘yan adawa domin tunawa da ranar haihuwar jam’iyyarsu ta SDF, shekaru ashirin da bakwai da suka gabata, an gudanar da taronne a jihar ‘yan awaren Ingilishin kasar bangaren dake ta kai ruwa rana da gwamnatin kasar.

Da kammala taronne jagoran ‘yan adawar kasar ya kama hanyarsa zuwa balaguro kasar Burtaniya. Maigali Ummaru, daya gdaga cikin mambobin kungiyar ya bayyanawa wakilin muryar Amurka cewar makasudin balaguron da shugaban nasu yayi zuwa Ingila, shine domin shirye shiyen da bangaren na Ingilishi, yak e wajan fara takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekarar 2018.

Malamin ya kara bayyana cewa kokarinsu shine su kafa sabuwar gwamnati domin shugaban kasar mai ci yanzu, Paul Biya, ya dade akan karagar mulkin kasar.

Dr Tony Massanin Harkokin siyasar kasar Kamaru ya bayyana cewa taron da jam’iyyar SDF, ta gudanar na nuna nkwazo ne domin kawo sauyi a gwamnatin kasar ta Kamaru.

Domin karin bayani ga rahoton Garba Awal daga Kamaru.

Your browser doesn’t support HTML5

Jam'iyyar Adawa A Jam'huriyar Kamaru Na Ci Gaba Da Fafutukar Neman Sauya Gwamnati