Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 26 A Misra


Hoton Motar Bas Din Da Aka Kaiwa Hari A Misra, May 26, 2017.
Hoton Motar Bas Din Da Aka Kaiwa Hari A Misra, May 26, 2017.

'Yan Bindiga dadi sun kashe kimanin Kiristoci yan darikar Aqbat 26 da kuma jikkata wasu kusan 25 a hanyarsu ta zuwa Jihar Minya, a Masar

Jami’ai a Masar sun bayyana cewa a yau Juma’a wasu yan bindigar da suka rufe fuskokinsu sun kai farmaki a kan wata motar bas dake dauke da kiristoci mabiya darikar Aqbat, ko Copt a turance, wadanda ke kan hanyar zuwa wata majami’a, suka kashe akalla 26 daga cikinsu.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Masar ta ce maharan su kimanin 10 a cikin wasu motocin a kori-kura guda uku, sun far ma wannan motar bas dake kan hanyar zuwa majami’ar Saint Samuel a Jihar Minya, wacce ke da nisan fiye da Kilomita 200 daga al-Qahira.

Gwamnan Jihar Minya Essam El-Bedawi ya fadawa tashar Talabijin ta kasar cewa, “Maharan sunyi amfani da makamai masu sarrafa kansu” yayin da tashar ta nuna hotunan Bus din da tagoginta sun farfashe, 'Yan sanda sun kewayeta da kuma motar Asibiti.

Kamar yadda ma’aikatar lafiya ta bayyana, kimanin mutane 25 ne suka jikkata a harin.

Har izuwa yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki alhakin wannan hari, duk da dai lamarin yayi kama da aikin Masu tsatstsauran ra’ayin Islam dake da alaka da ISIS na Masar, wadanda suka aiwatar da hare hare har biyu akan wadannan kiristoci ‘yan darikar Aqbat a watanni shida da suka gabata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG