Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Da Wasu Kasashen Afirka Zasu Takawa Masu Son Zuwa Turai Gudun Hijira Birki


An jawo hankalin duniya kan matsallar batun masu tsallaka teku domin isa turai

Yau shugabannin kasashen Afrika da dama suka shiga tattaunawar ranar karshe na taron kolin da ake na kasashen nan bakwai masu masana’antu da ake kira G-7, wanda ake gudanarwa a birnin Taormina na kasar Italiya.

A wajen wannan zaman na karshe, mai masaukin, Italiya, tana son janyo hankali ne ga matsalar da ake ci gaba da fuskanta ta samun dubban mutanen dake kokarin tsallaka tekun Mediterranean don isa nahiyar Turai don soma wata sabuwar rayuwa a can.

A kan haka ne shugabannin kasashen Ethiopia, Kenya, Nijar, Nigeria da Tunisia suka shiga tattaunawar ta yau da yake galibin duk mutanen dake kokarin yin wannan gudun hijiran ‘yan kasashensu ne.

Maganar kare muhalli na daya daga cikin manyan batutuwan da suka janyo muhawara mai zafin gaske a lokacin wannan taron kolin na bana na kasashen G-7, koda yake wakilan gwamnatocin Ingila da Amurka duk sun musanta cewa akwai wani sabani a tsakanin mahalarta taron.

Yayinda suke jiran Amurka ta yanke shawarar ko zata ci gaba tare da su, sauran kasashe shidda dake cikin kungiyar G-7 sun tabattarda cewa su kam suna nan daram akan shirinsu na ci gaba da bada muhimmanci ga yarjejeniyar da aka kulla a Paris kan kare muhalli.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG