Farfesa Abdullahi Yibaikwal Shehu ya bayyana hakan ne a yayin karbar bakuncin daliban su 107 tare da tawagar ofishin jakadancin Najeriya a Rasha a filin jiragen sama na kasa da kasa na Domodedovo dake birnin Moscow a ranakun farko-farkon watan disamban shekarar 2022.
Daliban Najeriya kimanin 107 da suka samu tallafin karatu a kasar Rasha na shirye-shiryen fara karatu a fannonin aikin likitanci da injiniya na shekarar 2022 zuwa 2023.
Tsarin karatun na zama wani bangare na yarjejeniyar karatu da aka kulla tsakanin Najeriya da tsohuwar Tarayyar Soviet tun shekarar 1960, inda kasashen biyu suka ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar da kuma sabunta ta har wannan lokaci.
Da yake maraba da daliban, jakadan Najeriya a Rasha Farfesa Abdullahi Yibaikwal Shehu, ya taya daliban murnar samun wannan dama ta isa Moscow babban birnin kasar Rasha, ya na mai jan hakalinsu da su kasance masu bin dokokin kasar ta Rasha.
Ambasada Abdullahi Yibaikwal ya bayyana cewa samun nasarar karatu a kasar Rasha da daliban suka yi na nuna irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a fannin ilimi.
Farfesa Shehu ya tabbatar wa daliban cewa ofishin jakadancin Najeriya zai ba wa daliban dukkan wata gudunmuwa har su kammala karatunsu cikin nasara.
Tun a shekarar 1960 ne kasashen Najeriya da Rasha suka kulla yarjejeniya a fannin ilimi wacce ake yi wa take da yarjejeniyar ilimi ta Najeriya ta bai daya, wato Nigerian Bilateral Education Agreement BEA a turance, sannan aka sauya wa yarjejeniyar fasali a shekarar 1997.
Tun daga wancan lokacin, kasar Rasha ta ringa daukar nauyin daliban Najeriya domin yin karatu a fannin kimiyya da fasada, aikin likita da na injiniya.
Farfesa Shehu ya shaida wa daliban cewa ba su da wata fargaba yayin zamansu a Rasha domin suna cikin tabbataccen aminci, kariya da zaman lafiya.
Sai dai ya ja hankalinsu da cewa dole ne su zama masu da’a, sannan su san irin mutanen da za su ringa yin mu’amala da su a yayin karatunsu don gudun abun da ka je ya dawo.
Tafiyar daliban dai a wannan karon na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yaki tsakanin kasashen Ukraine da Rasha, inda dakarun Rasha suka mamaye wasu yankunan kasar ta Ukrainę saidai a baya-bayan nan an dan tsagaita Wuta.
Kasar ta Rasha dai na kara fuskantar matsin lamba da mai da ita saniyar ware daga kasashen yammacin duniya kan yakin da take yi da kasar Ukraine.
A lokacin da aka fara yakin dai, daruruwan daliban Najeriya dake karatu a kasar ta Ukraine suka dawo gida Najeriya, kasancewar yakin ya shafi wasu yankunan da suke, da kuma fargabar kar yakin ya kai ga inda wasu suke domin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu.