Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine-Jirgi Na Uku Ya Dawo Da Rukunin ‘Yan Najeriya


Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

Jirgi na uku dauke da ‘yan Najeriya da ke ficewa daga Ukraine don tsira daga mamayar Rasha, ya isa filin saukar jiragen sama na Abuja.

ABUJA,NIGERIA -Jirgin dauke da ‘yan Najeriya 174 ya taso ne daga kasar Hungary, da ke daya daga kasashen da ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashe su ka fake kafin dawo da su gida ko kasashen daban-daban.

Wannan jirgin dai na kamfanin AIR PEACE ne da ke cikin kamfanoni biyu da su ka hada da MAX da gwamnati ta yi shata don kwaso ‘yan Najeriya musamman dalibai da adadin su ya kai 5000.

An samu tabbacin zuwa yanzu akwai ‘yan Najeriya da ba sa sha’awar dawowa gida don fatar da su ke da ita cewa nan gaba lamura za su daidaita su koma karatu ko harkokin su.

Gwamnatin Najeriya ta ware dala miliyan 8.5 don gudanar da wannan jigila da kula da lamuran abinci da sauran bukatu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG