Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Yemen, ya nuna matukar damuwarsa a yau Alhamis, kan yadda ake kara samun tashin hankali a Yemen, amma kuma ya yi maraba da alkawarin da dakarun da Saudiyya ke jagoranta suka yi, na cewa za su bari a kai kayan agaji a wani muhimmin yanki.
A ranar Talata, Isma’ila Ould Cheikh Ahmed, ya yi Allah wadai da harin makami mai linzami da ‘ya tawayen Houthi suka kai akan Saudiyya, yana mai cewa harin zai iya wargaza shirin zaman lafiyan da aka shimfida a Yemen.
Bayan da ‘yan tawayen suka harba makamin akan wani filin tashin jirage da ke Birnin Riyadh a watan Nuwamba, kasar ta Saudiya ta girke wani shinge a sama da kan teku a Yemen na tsawon wasu makwanni, tana mai cewa daukan wannan mataki ya zama dole domin a dakile safarar makamai da ake yi.
Amma duk da harin na watan Nuwamba, a jiya Laraba dakarun hadin gwiwa da Saudiyan ke jagoranta sun ce, za su bar tashar jiragen ruwa ta Hodeida a bude, har na tsawon kwanaki 30, domin a samu damar aikawa da kayayyakin abinci da sauran kayan agaji.