Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Gawawwakin Mutante Goma A Rohingya


Yanghee Lee
Yanghee Lee

An gano wasu gawwaki goma a wani rami guda a Rohingya, sanadiyyar tashe tashen hankulan da suka auku a yankin inda 'yan sanda ke azabtar da musulman yankin.

Jakadiya ta musamman mai kula da hakkokin jama’a a Myanmar, ta ce gwamnatin Myanmar, na hana ta kai ziyara kasar don duba halin da jama ke ciki a kasar dake gabashin Nahiyar Asiya.

Sanarwar jakadiyar ta musamman Yanghee Lee, na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Myanmar, suka gano gawarwakin mutane 10 a wani rami a arewa maso yammacin jihar Rakhine, inda garuruwan musulmin Rohingya, fiye da 600,000 suke kafin su gudu zuwa makwabciyar kasar Bangladesh, don gujewa kuntatawar da sojojin kasar suke yi masu.

Ranar litinin ne aka gano ramin a wani kauye mai suna Inn Din. Rundunar sojan kasar ta ce tana bincike akan lamarin.

Ms. Lee wadda aka haifa a Koriya ta kudu ta ce ta yi mamaki kuma ba ta ji dadin matakin gwamnatin kasar ba, wanda ke nuna cewa tabbas akwai wani mummunan abu dake faruwa a Rakhine.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG