Jakadan Faransa a Nijar ya bar birnin Yamai da sanyin safiyar Laraba, kusan wata guda bayan da gwamnatin mulkin sojan kasar ta ba da umarnin korar shi, kuma 'yan kwanaki bayan da shugaba Emmanuel Macron ya ce zai janye jami’in diflomasiyyar tare da sojojin Faransa.
Dangantaka tsakanin Nijar da Faransa, tsohuwar kasar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka a baya, wadda ke da rundunar soji a kasar don taimaka wa a yaki da masu ikirarin jihadi, ta tabarbare tun bayan da hafsoshin sojojin kasar suka kwace mulki a Yamai a watan Yuli.
Majalisar mulkin sojan dai ta umarci jakadan Faransa Sylvain Itte da ya fice daga kasar cikin sa'o'i 48 a karshen watan Agusta, a zaman martani ga abin da suka bayyana a matsayin matakin da Faransa ta dauka wanda ya saba wa muradun Nijar.
Da farko Faransa ta yi watsi da wannan umarni, inda ta tsaya kan matsayinta na cewa gwamnatin mulkin sojan ba ta bisa doka, tana mai kira da a maido da zababben shugaban kasa Mohamed Bazoum, wanda aka hambarar a juyin mulkin watan Yuli.
Amma Macron ya sanar a ranar Lahadin da ta gabata cewa jakadan zai koma birnin Paris, kuma sojojin Faransa za su fice daga kasar da ke yankin yammacin Afrika zuwa karshen shekarar 2023.