Jakadan Falasdinu A MDD Ya Zargi Isra'ila Da Ci Gaba Da Take Dokokin Kasa Da Kasa

Jakadan Falasdinu A MDD Riyad Mansour

Wakilan Falasdinu a MDD na ci gaba da matsawa kwamitin sulhun MDD ya dauki mataki akan kasar Isra’ila idan taci gaba da nacewa da gina gidajen Yahudawa a yankunan da Falasdinawa ke son anfani da su wajen girka kasarsu wata rana.

Jakadan Falasdinu a MDD din, Riyad Mansour, ya zargi Israila da ci gaba da take dokokin kasa da kasa.

Yace takaita harkokin gina gidajen Yahudawan Israila da kuma janyewa daga yankunan Palasdinu, wajibi ne wurin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Palasdinu da Israila.

Jakadan Israila a majalisar, Danny Danon bai tabo maganar gidajen bani-Yahudu ba a cikin jawabinsa ga kwamitin sulhun, sai dai ya la’anci abinda ya kira mataki na bangare daya da za a dauka a kan Israila.

A cikin yakin 1967 ne Israila dai ta kama yankin Yammacin kogin Jordan daga bisani ta mamaye baki dayan Kudus, a bisa hujjar cewa tana da yancin gini a wurin don tabbatar da tsaron kasarta.