Kungiyoyin Addinin Musulumci a kasashen Afirka, sun fara kushe matakin da kasar Chadi, ta dauka na haramta Nikab ko Hijab a kasar.
Gwamnatin kasar ta Chadi dai ta dauki wannan matakin ne a matsayin matakin tsaro biyo bayan wani harin kunar bakin wake da ya hallaka jama’a, a kasar ta Chadi, a cikin makon jiya.
Kungiyar Izala na daya daga cikin kungiyoyin dake gudanar da wa’azin Musulumci a kasashen Afirka, ta yamma, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikum, wanda yake shine mataimakin shugaban Malaman kungiyar a Najeriya, yace “ Duniya fa yau abun da ake tutiya dashi Demokradiya, to idan har demokradiya, ake yi a duniya to danme wasu mutane zasu dauki Nikabi ko Hijabi, suce salo ne da tsari irin na gudanar da addinin su, sanan wata Gwamnati tace zata hana su, idan anyi haka inna demokradiyar take.”
Ya furta haka ne a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a wajen bude Tafsirin watan Ramadan a garin Minna, fadar Gwamnatin jihar Neja.