Lafiya uwajjiki, sai da lafiya ake gudanar da halin yau da kullun, Hadiza Ado, wata matashiyace wadda take ganin yakamata ta taimakama ‘yan uwanta mata wajen morema gidan aure.
Hadiza, dai ta kasance mace mai sha’awar ganin cewar kowace mace ta samu duk jin dadin da yakamata ace kowace mace tasamu a lokacin aurenta, a zaman takewar ta da mijinta, don haka sai ta fara sana’ar “Tsimi” ita dai wannan sana’ar tana hada wasu itatuwane da kuma wasu magunguna, wanda idan mace zatayi aure sai a bata tasha kuma tayi wanka da shi, wanda zai gyara mata jikinta, har da zai sa mijinta ba zaiyi sha’awar kara wani aure ba, a sanadiyyar kyautatawa da yake samu daga matarsa.
Akwai bukatar kowace yarinya da za’a kaita gidan miji a tsimata, don ta kara samun lafiya, suma mata wadanda suka kwana biyu da aure suna da bukatar irin wannan tsimin, don zai taimaka musu wajen gyaran jiki da zai kauda duk wata hatsaniya a cikin gidan aure.
Ita dai Hadiza, ta kamala karatun ta na dipilona, kuma ita ‘yar shekaru 22 ce, wanda take kara kira ga mata matasa da su tashi su dukufa wajen neman abunyi, wanda ta haka zasu iya taimakama kansu da ma wasu mata ‘yan’uwansu, don haka kowace tayi amfani da baiwar da Allah yayi mata ta kirkiro wata sana’a da zata iya taimakama wasu kuma ta iya dogaro da kanta.