Iyayen yaran da aka sace a jihar Yobe dake arewacin Najeriya wadanda suka ce yaran su da yawan su yakai 100 da ‘yan Boko Haram suka sace suna kara shiga cikin halin bakin ciki da damuwa.
Jami’an gwamnatin jihar ta Yobe da suka ce ‘yaran da aka sace 50 daga cikin su babu wani labara game dasu.
A ranar littini da yammaci ne dai aka kaiwa wannan makarantar mata ta garin Dapchi dake cikn jihar ta Yobe hari.
Kuma tun daga wannan lokacin ake ta samun bayanai da suke ta karo da juna akan yara nawa ne har yanzu ba a gani da kuma wai shin nawa ne aka sace gaba daya.
Da farko ma jami’an ‘yan sanda da na ma’aikatasr ilmi na yankin cewa suka yi ba wasu dalibai da aka sace, illa kawai suna cikn daji ne suna boyewa bayan da aka kai musu hari.
Dama dai jami’an gwamnatin Najeriya sau tari irin haka ta faru domin basu faye bada bayanai sahihai ba.
Idan dai ba a manta ba a ranar Laraba ne sojojin Najeriya suka ce sun samu nasarar kwato yaran har su 76.
Amma kwaran sai a jiya sailin da gwamnanjihar Ibrahim Gaidam ya ziyarci makarantar a ziyarar gani da ido sai kuma ya shaidawa iyayen yaran cewa ba gaskiya ba ne labarin da sojojin Najeriya suka bayar na cewa sun samu nasarar kwato yaran ashe ko guda basu kwato ba.
A cikin sakon da ya aika a shafinsa na Twitter ranar Laraba, shugaba Muhamadu Buhari yace gwamnati za ta yi duk abinda ya dace na ganin an kwato yaran nan da suka bata.’’Yace ba shakka ina cike da bakin ciki tare da bin sahun iyayen yaran da ba a ga ‘yayan su ba”.Yace amma yana mai basu tabbacin cewa “za mu yi duk abinda ya dace mu yi na ganin ‘ya’yan wadanda ba a gani ba suma sun dawo wurin iyayen su”.
Gwamnatin tarayyar Najeriya dai tasha fadin cewa ta gama da kungiyar Boko Haram amma har kullun sai aikata barna suke yi, musammam ma kai harin kunar bakin wake.
Domin karin bayani a saurari wannan rahoto na Haruna Dauda
Your browser doesn’t support HTML5