Matsalar kula da maruya a kasashe masu tasowa musamman ma a Afirka, wani babban kalubale ne da iyaye, musamman mata ke fuskanta.
A lokuta da dama, idan mahaifi ya rasu, ya bar ‘ya’ya, uwar kan shiga mawuyacin hali wajen kula da wadannan yara ta fuskoki daban-daban.
A Jihar Agadez da ke Jamhuriyar Nijar, akwai mata da dama da suka tsinci kansu a cikin irin wannan kangi na kula da marayu.
“Dangin uba, babu wanda ya taba lekowa, ya ce ga shi ko da kwayar hatsi daya, ki taimaka wa yaran nan.” Inji wata da majinta ya rasu ya bar mata ‘ya’ya, wacce kuma ta nemi a sakaya sunanta.
“Yau idan aka ce mijinka ya fadi ya mutu, sai dai ka kai kukanka ga Allah.” Wata mata ta biyu ta fadawa wakiliyarmu Tamar Abari.
Labarin wadannan mata, kadan ne daga cikin dumbin iyaye da ke fuskantar irin wannan matsala.
Sai dai akan samun daidaikun kungiyoyi da kan tallafawa irin wadannan mata wajen kula da marayun.
“Maraya yana bukatar taimako, musamman ma a nan jihar Agadez, ba taimako na ka bashi kudi ba, ka taimaka ka sa shi a hanya ta kwarai.” Inji Mamman Albishir, wakili a kungiyar HAI, da ke taikamawa marayu a jihar ta Agadez.
Saurari cikakken rahoton Tamar Abari domin jin karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5