Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko An Samu Sultan A Maradi


Sultan din Maradi Alhaji Ado Zaki
Sultan din Maradi Alhaji Ado Zaki

A karon farko tun lokacin da aka kafa sarautar Maradi a shekarar 1807, yanzu Faransa ta daga sarkin garin suwa matsayin Sultan din Katsinan Maradi a wani gagarumin biki a garin na Maradi inda Jakadan Faransa ya kasance ya kuma mika wa sabon Sultan din sandar girma.

An nada Alhaji Ado Zaki a matsayin Sultan din Katsinan Maradi a karon farko a tarihin garin tun lokacin da aka kafa garin a shekarar 1807.

A jerin sarakuna sabon Sultan din Katsinan Maradi shi ne na 23. Malam Yusuf Abu Magaji malamin tarihi ne kuma ya yi bayani. A cewarsa duk inda Faransa ta ga kwazo tana karawa sarautar girma. Dalili ke nan ta karawa Alhaji Ado Zaki ya zama Sultan din Katsinan Maradi. Faransa ce ta nadashi.

Murna ce ta arziki wadda ta dade tsakanin kasashen Faransa da Nijar kuma duk abun da Faransa zata yi tana yi ne da sarakunan kasar kamar yadda Jakadan kasar Faransa dake Nijar ya yi bayani.

A saurari rahoton Mani Chouaibu domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG