Iyalan Rayshard Na Kira Da a Yi Sauyi A Fannin Ayyukan 'Yan Sanda

Yadda masu zanga zanga suka bazama a birnin Atlanta domin nuna fushinsu kan kisan Rayshard Brooks. Ranar 15, 06, 2020. Mandatory Credit: Alex Hicks Jr.-USA TODAY NETWORK

Iyalan bakar fatar nan da ‘yan sanda suka harbe har lahira a garin Atlanta da ke kudancin Amurka sun yi kira da a yi sauye-sauye a fannin ayyukan dan sanda.

Sun yi kiran ne a jiya Litinin bayan wannan harbi da ya faru a wani wajen sayar da abinci a ranar Juma’ar da ta gabata.

Mutuwar Rayshard Brooks dan shekara 27 da haihuwa, wanda ma’aikacin gidan sayar da abinci ne kuma mahaifin ‘yan mata yara 3, ita ce kisa ta baya-bayan nan da ta auku akan wani ba’amurke bakar fata.

Ta kuma kara dasa alamar tambaya kan yadda ‘yan sanda ke amfani da karfin da ya wuce kima inda har ta haddasa zanga zanga a sassan Amurka.

"Babu wani hukunci da za a yi da zai saka ni na yi farin ciki akan abin da ya faru domin mai gidanta ba zai taba dawowa ba.” In ji matar Brooks, Tomika Miller.

Ofishin kula da ayyukan kiwon lafiya a karamar hukumar Fulton ya ayyana mutuwar Brooks a matsayin kisan-kai, sannan binciken gano musabbabin mutuwarsa ya nuna cewa an harbe shi ne sau biyu a baya.