Italiya Ta Lashe Kofin Euro 2020 Bayan Doke Ingila a Bugun Fenariti

'Yan Wasan Italiya lokacin da suka daga kofin Euro 2020.

Kafin wasan ya je ga matakin bugun fenaritin, Ingila ce ta fara sammakon zura kwallo a ragar Italiya, abin da ya ba ta damar mallake wasan gabanin a je hutun rabin lokaci.

Faretin Bas Na Italiya Euro 2020 A Titunan Rome

Your browser doesn’t support HTML5

Faretin Bas Na Italiya Euro 2020 A Titunan Rome

Italiya ta lashe kofin gasar Euro 2020 bayan da ta doke Ingila a bugun fenariti da ci 3-2.

Wasan ya kai matakin fenaritin ne bayan da kasashen biyu suka yi kunnen doki da ci 1-1, lamarin da ya sa aka kara lokaci kafin a je ga bugun daga kai-sai-mai tsaron-gida.

Kafin wasan ya je ga matakin bugun fenaritin, Ingila ce ta fara sammakon zura kwallo a ragar Italiya, abin da ya ba ta damar mallake wasan gabanin a je hutun rabin lokaci.

Dan wasan Ingila Luke Shaw da ke buga kwallo a Manchester United ya narka kwallon ta wuce ragar Gianluigi Donnarumma, minti biyu kacal da fara wasan wanda aka buga a filin Wembley da ke London.

Sai dai dan wasan Italiya Leonardo Bonucci ya farke kwallon a minti na 66, lamarin da ya sa wasan ya koma danye.

‘Yan wasan Roberto Mancini sun yi ta nuna alamun dari-dari a farkon wasan, amma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sun yi ta kai hare-hare.

Wannan shi ne karo na uku da Italiya take lashe kofin gasar, wacce Ingila ba ta taba dauka ba.

Kiyasin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar a ranar 27 ga watan Mayu ya nuna cewa Ingila ce ta hudu a iya taka leda a duniya yayin da Italiya take mataki na 7.