Isra’ila Ta Sanar Da Kisan Jagoran Hezbollah Sayyed Hassan Nasrallah

Dakarun Isra'ila

A ranar Asabar din nan Isra’ila ta sanar da cewa ta kashe jagoran Hezbollah, Sayyed Hassan Nasrallah, wanda ya jagoranci kungiyar da ta kwashe gwamman shekaru ta na rikici da Isra’ila, da kula da sauya sigar ta zuwa wata rundunar dakarun soji da tayi karfin gaske tsakanin fitattun yankunan Larabawa a tsawon lokaci, da ke samun goyon bayan Iran.

Har yanzu dai kungiyar Hezbollah da Iran ke marawa baya, ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da Nasrallah, wanda ya jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 32.

Rundunar sojin Isra’ila tace, ta kashe Nasrallah ne a wani hari ta sama da ta kai kan hedikwatar kungiyar da ke yankin kudancin Beirut a kwana guda da ya gabata.

Mai Magana da yawun sojin Isra’ila Avichav Adraee ya rubuta cikin wata sanarwa a shafin sadarwar zamani na X cewa, sojoji sun kawar da jagoran kungiyar Hezbollah Hassan Nasrallah.

Kungiyar ta Hezbollah ta tabbatar da ikirarin da Isra’ilan tayi na kisan Nasrallah, inda a yanzu, mabiyan shi za su rika tunawa da shi a matsayin wanda ya yi tsayuwar daka da Isra’ila ya kuma ki, ya bada kai bori ya hau ga Amurka. Ga makiyan shi kuwa, shugaba ne shi na kungiyar ta’addanci, kuma wani makwafi ga akidar shi’ar musulunci ta Iran, a tatagurzar da ta ke yi na samun wurin zama a yankin Gabas ta tsakiya.