Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahmoud Abbas Ya Kalubalanci Amurka Kan Makaman Da Take Ba Isra'ila


Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas

Ya kara da cewa "Bai kamata a ci gaba da wannan haukar ba. Daukacin duniya na da alhaki akan abin da ke faruwa ga mutanen mu a Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya yi kira ga kasashen duniya a zauren Majalisar Dinkin Duniya na 79 a ranar Alhamis, musamman ma Amurka, da ta daina aikawa Isra'ila makamai domin kawo karshen zubar da jinin da ake yi a yammacin Kogin Jordan da Gaza.

Abbas ya yi wannan kiran ne, a yayin da yake gabatar da jawabinsa a babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya na shekara-shekara dake gudana a Amurka.

Cikin harshen Larabci, Abbas ya ce, “A daina aikata wannan laifin. A dakatar da shi yanzu. A daina kashe yara da mata. A daina kisan kare dangi. A daina aika makamai zuwa Isira’ila."

Ya kara da cewa "Bai kamata a ci gaba da wannan haukar ba. Daukacin duniya na da alhaki akan abin da ke faruwa ga mutanen mu a Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan.”

Jakadan Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya Danny Danon, ya kwashe tsawon mintuna 26 yana sukar jawabin na Abbas, na rashin ambaton kalmar Hamas ba, ba tare da yin la’akari da muhimmiyar rawar da kungiyar take takawa wajen ruruta wutar rikicin ba.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG