Isra'ila Ta kwace Ikon Wani Yanki Na Tuddan Golan

Wadansu 'yan kasar Syria suna kokari ketara kan iyaka

Da yake bayani dangane da lamarin, Firai Ministan Isra’ila Gideon Saar ya ce, Isra’ila ta damu matuka cewa wasu makaman Syria na iya fadawa hannun wadanda ke son cutar da kasar Yahudawa.

“Shi ya sa muka kai hari kan muhimman wuraren da za su iya zama makamai kamar, misali, sauran makamai masu guba ko makamai masu linzami masu cin dogon zango da rokoki domin kada su fada hannun masu tsattsauran ra'ayi."

Ya yi magana ne bayan da sojojin Isra'ila suka karbe wani yankin da ba a musayar wuta tsakanin Isra'ila da Siriya.

Firayim Ministan Isra'ila ya ce Isra'ila ba za ta bari duk wata runduna da take gaba da Isra’ila ta kafa kanta a kan iyakar Isra'ila ba.

Kan iyakar Syria da Isra'ila

Sai dai manazarta Isra'ilawa sun ce Isra'ila na kallon abubuwan da ke faruwa a kasar Siriya a matsayin wani batu na cikin gida na al'ummar Siriya, kuma tana fatan jagoran 'yan tawaye Abu Mohammed al-Golani zai iya kulla dangantaka da Isra'ila.

"Na san zahiri cewa Isra'ila tana da wannan alaka da Kurdawa a Siriya. Sun tuntubi gwamnatin Isra'ila sun ce za su ba da hadin kai. Don haka Kurdawa da kuma Druze a tuddan Golan na Siriya su ma suna aikewa da sakonni iri iri na zaman lafiya ga Isra'ila ."

Iyakar da ke tsakanin Isra'ila da Siriya ta kasance iyakar Isra'ila mafi kwanciyar hankali na tsawon shekara da shekaru, sakamakon yarjejeniyar da aka cimma bayan yakin Yom Kippur na 1973. Sai dai wasu manazarta sun ce sabon yanayin zai iya kai ga cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Siriya.

Yan kasar Syria da ke Turkiya suan jira su ketara ka iyaka.

Hazem Alghabra wani manazarci dan kasar Syria kuma wanda ya kafa wata cibiyar tuntuba a Washington da ake kira Frontiers Consultants ya bayyana cewa, Isra'ila za ta iya zama mai ikon fada a ji a yankin.

"Ina kokakarin fahimtar ko mutanen da Siriya, suna shirye su karbi taimako daga Isra'ila, watakila nan gaba kuma su fara huldar kasuwanci da Isra’ila. Ina tsammanin yana za a yi gaggawa idana aka yanke hukumcin hakan. Amma na yi imani cewa, Isra'ila tana kan hanyar zama mai ikon fada a ji a yankin, akalla haka lamarin ya ke yanzu ta hanyar soja. "

Isra'ila ta zuba ido don ganin yadda Iran za ta mayar da martani kan abubuwan da suka faru a Siriya.

Manazarta na Isra'ila sun yi imanin cewa, Iran ta raunana saboda murkushe kungiyar Hizbullah a kudancin Lebanon da kuma abubuwan da suka faru a Siriya.

Wasu a Isra'ila na fargabar cewa, Iran na iya kokarin sake maida hannun agogo ta hanyar ci gaba da shirinta na nukiliya, wanda zai iya kai ga Isra'ila ta kai wa Iran hari.

Ku Duba Wannan Ma Martanin 'Yan Siriya Mazauna Turai Kan Hambarar Da Gwamnatin Bashar al-Assad