Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a yankin Gaza da ke karkashin kulawar Hamas a ranar Juma’a bayan gaza tsawaita matsayar da aka cimma ta dakatar da bude wuta a baya.
Ma’aikatar lafiya a Gaza ta ruwaito cewa akalla Falasdinawa 178 aka kashe yayin da wasu 589 suka jikkata.
Dakarun Isra’ila sun ce sojojinsu na kasa da na sama da kuma na ruwa sun kai hari a wurare sama da 200 da suka kira maboyar mayakan Hamas tun bayan da wannan yarjejeniya ta zo karshe.
Yankin da ake kira Khan Younis da ke kudancin Gaza ya yi fama da hare-haren Isra’ila, lamarin da ya sa mazauna yankin suka yi ta neman mafaka a cewar wani dan jaridar Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters da ke wurin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce barkewar sabon fadan zai kara ta’azzara matsalar matsananciyar rayuwa da haifar da kalubale ga ayyukan jin-kai da ake yi a yankin.
Isra’ila da Hamas na zargin juna da gaza sabunta yarjejeniyar, ko da yake, Fadar White House ta dora laifin akan Hamas wacce ta gaza ba da sabon jerin sunayen mutane da za ta sako, wanda hakan sharadi ne da yarjejeniyar ta kunsa kafin a sabunta ta.