Isra'ila ta fadada yakinta da mayakan Hezbollah a Lebanon a ranar Litinin, inda ta kashe akalla mutum 490 sannan ta jikkata wasu sama da 1,650 a wasu munanan hare-haren sama da suka haifar da fargaba akan yiwuwar ya kai ga yakin fito-na-fito.
Sojojin Isra'ila sun ce sun auna sama da wurare 1,300, yayin da kafar yada labaran Lenanon kuma ta ba da rahoton manyan hare-hare a fadin wasu wurare a yankun kudancin kaşar.
Daga cikin wadanda aka kashe har da yara 35 da mata 58, a cewar jami'an Lafiyar Lebanon.
Sojojin Isra'ila sun gargadi sun yi wa mazauna yankin Bekaa da ke kwarin gabashin Lebanon su nesanci ma’adanan makaman Hezbollah.
Cikin wani sakon sauti da Firan Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya aikewa fararen hular Lebanon, ya bukace su da su yi biyayya ga umarnin Isra’ila su fice, yana mai cewa “su kiyaye wannan gargadin”.
“Don Allah ku kauce wa tashin hankali yanzu”, in ji Netanyahu. “Da zarar mun kammala kai hare harenmu, za ku iya koma wa gidajenku lami lafiya. Dubban mutane ne sun gudu daga kudancin Lebanon, wanda ya haifar da cunkoson motoci akan manyan titunan Beirut.#