Isra’ila ta sake kaddamar da wasu jerin hare-hare a birnin Lebanon cikin dare, inda ta ce ta sake nasarar halaka wani kwamandan kungiyar Hezbollah kwanaki bayan halaka shugabanta Hassan Nasarallah.
Har zuwa wayewar garin Lahadi, ana ci gaba da ganin tashin hayaki a wani dogon bene tun bayan harin sama da Isra’ila ta kai a Beirut a ranar Juma’a.
Dakarun Isra’ila sun ce hare-haren nasu sun kaikaici shugaban kungiyar Hebollah da Amurka ta ayyana a matsayin dan ‘dan ta’adda ne.
A ranar Asabar kungiyar ta tabbatar da mutuwar Hassan Nasarallah wanda ke jagorantar Hezbollah.
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kwatanta Nasarallah a matsayin wanda ya kuduri aniyyar ganin bayan Isra’ila.
“Nasarallah ba wani ba ne illa dan ta’adda. Shi ne ginshikin makirce-makircen kasar Iran. Shi da mutanensa sun kuduri aniyyar ganin bayan Isra’ila.” In ji Benjamin Netanyahu.
A halin da ake ciki Iran wacce ita ce babbar kawar Hezbollah, ta sa an dasa bakar tuta a ginin babban masallacin Imam Reza bayan mutuwar Nasarallah.
Matakin saka wannan alama da Iran ta yi, na zuwa ne yayin da ita ma kungiyar ta Hezbollah ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa “Nasarallah ya tafi wajen wadanda suka yi shahada” tana mai “shan alwashin ci gaba da yaki da makiya da kuma nuna goyon baya ga Falasdinu.”
Yayin da daruruwan iyalai ke kwanciya a kan titunan Beirut hukumomin kasar ta Lebanon sun ce mutanen da suka rasa muhallansu sun kai miliyan daya.
Dakarun tsaron Isra’ila sun fitar da wasu jerin hotunan bidiyo wadanda suke nuna “yadda aka kai dozin-dozin din hare-hare akan maboyar Hezbollah a Lebanon.”
Isra’ila dai ta ce ta yi gargadi fararen hul da su fice daga yankin
Sai dai Firaiministan Lebanion na rikon kwayra Najib Mikati yayin wata hira da gidan talabijin na Tele Liban ya caccaki Isra’ila.
“Abin takaici shi ne dokar da take kare rashin adalci a duniya ta ba Isra’ila damar yin fatali da duk wani yunkuri da ake yi na cimma matsayar tsagaita wuta a yakinta da Lebanon, sabod aita Isra’ila babu abin da ya sha mata kai da wata doka ko ‘yancin gashin kan kasa.” Mikati ya ce.
An ci gaba da ganin hare-haren cikin daren krshen makon da ya gabata a Beirut, lamarin da ya jefa jama’a cikin zullumin abin da kai ya biyo baya.
A gefe guda kuma daruruwan masu zanga-zanga a birnin Bagadaza sun yi bore kan kisan Nasarallah inda suka yi yunkurin kutsawa cikin yankin Green Zone a Iraqi da ke da dauke da ofishin jakadancin Amurka.
Kakaki a Fadar White House John Kirby a ranar Lahadi ya fada a shirin “This Week’ na gidan talabijin na ABC kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X cewa Amurka na bibiyar dukkan abubuwan da ke wakana.
“Muna kallon dukkan abubuwan da ke faruwa, ko Hezbollah ko Iran za su mayar da martani da sauran kungiyoyi da ke Iraqi da Syria. Yazama dole mu zauna cikin shiri, kuma a shirye muke.” In ji Kirby.
Ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce sama da mutum dubu daya ne suka mutu yayin da aka jikkata dubu shida cikin makonnin biyun da suka gabata.
Bayanai sun yi nuni da cewa, an kuma kashe mataimakin kwamandan dakarun juyin juya halin Musulinci na Iran Abbas Nilforoushan a harin da aka kashe shugaban kungiyar Hezbullah a Beirut.