Firai ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Talata cewa sojojin kasarsa sun kashe wanda ake sa ran zai gaji shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a wani hari da Isra’ila ta kai birnin Beirut a ranar 27 ga watan Satumba.
Hashem Safieddine, dan uwan ne ga Nasrallah kuma babban jami’in kungiyar ne da ake sa ran zai maye gurbin Nasrallah.
“Mun kashe dubban ‘yan ta’adda, cikin har shi Nasrallah, da wanda zai maye gurbin Nasrallah da kuma wanda zai maye gurbi sa. A yau, Hezbollah ba ta da karfin da take da shi shekaru da dama.” Netanyahu ya ce.
Tun makon da ya wuce dai ba’a sake jin duriyar Safieddine ba, a lokaci da Isra’ila ta kaddamar da jerin wasu hare-hare ta sama a wajen birnin Beirut inda nan ne wurin da Hezbollah ke da karfi sosai.
Har yanzu dai babu wani martani daga Hezollah, wacce yawanci take tabbatar da mutuwar manyan jami’anta.