Kungiyar ISIS mai fafutukar kafa daular musulunci a kasashen Syria da Iraqi, ta amince da mubaya’ar da kungiyar Boko Haram ta yi ga kungiyar, wacce ke ta-da kayar baya a Najeriya.
A wani faifai da ISIS ta fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, Kakakin kungiyar, Abu Mohammaed al-Adnani, ya yi maraba da wannan mubaya’a da kungiyar ta Boko Haram ta yi, ya na mai cewa hakan na nufin ayyukan kungiyar na kara fadada zuwa yankin Yammacin Afrika.
A cikin faifan, mai magana da yawun kungiyar ya ce Khalifa ya amince da wannan mubaya’a, ya na kuma taya abokanansu na Jihadi da ke Yammacin Afrika murna.
A makon da ya gabata ne shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mika wuya ga kungiyar ta ISIS, inda ya ce a shirye su ke su bi duk umurnin da ISIS za ta ba su.
Babu dai masaniya game da irin yadda kungiyoyo biyu za su dinga hada kansu.
Ko a baya ma wasu kungiyoyin jihadi da ke sauran sassan duniya sun yi mubaya’a da kungiyar ta ISIS, ko da ya ke a lokuta da dama wasu na ganin hadin kan kungiyoyin na fatar-baki ne kawai da bai shige nuna wasu alamu kamar bayyana tutoci.
A wata hira da ya yi da VOA a farkon makon nan ne Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya bayyana cewa ‘ya’yan kungiyar ta Boko Haram na samun horo daga kungiyar ta ISIS ne.