Ireland, Spain Da Norway Sun Amince Da Kafa Kasar Falasdinu

Ireland's Prime Minister Simon Harris (C), flanked by Ireland's Minister of Foreign Affairs Michel Martin (R) and Ireland's Minister for Transport Eamon Ryan (L), delivers a speech during a press conference, to recognise the state of Palestine at the Gove

Firaministan Spain Pedro Sanchez ya ce an dauki matakin ne da nufin kara kaimi wajen ganin an tsagaita bude wuta a yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza.

A yau Laraba ne Ireland da Spain da Norway suka sanar da amincewar su kan kafa kasar Falasdinu a ranar 28 ga watan Mayu, suna masu fatan sauran kasashen yammacin duniya za su yi koyi da shi.

Sai dai wannan lamarin ya yi tilasta wa Isra’ila janye jakadunta daga kasashen.

Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Israel Katz, ya ba da umarnin janye jakadun Isra'ila nan take domin tuntubar juna tare da yin gargadin cewa za a iya samun sakamako mai tsanani.

Israel Katz

"Ina aika sako karara a yau cewa: Isra'ila ba za ta yi kasa a gwiwa ba kan masu zagon kasa ga ikonta da kuma kawo barazana ga tsaronta." In ji shi.

Firai Ministan Spain Pedro Sanchez ya ce an dauki matakin ne da nufin kara kaimi wajen ganin an tsagaita bude wuta a yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a Gaza.

Shima Minista harkokin wajen Ireland, Micheál Martin, da yake magana dangane da lamarin, ya ce ''a yau mun bayyana karara ba tare da kumbiya-kumbiya ba za mu nuna goyon bayanmu game da 'yancin tsaro da na mutuntawa da gashin kai ga mutanen kasashen Falasdinu da Isra'ila''.

Micheál Martin

A nashi bangaren, Firai Ministan Spaniya, Pedro Sanchez, ya ce takwararsa a Isra'ila Benjamin Netanyahu ''yayi kunnen kashi, inda yake ci gaba da kai hare-haren boma-bomai kan asibitoci da makarantu tare da azabtar da mata da kananan yara da yunwa da kuma tsananin sanyi''.

Pedro Sanchez

A nasa bangare Firai Ministan Ireland, ya ce ''samun yancin ƙasashen biyu shi ne kawai mafita a kokarin samar da zaman lafiya''.

Kasashen duniya da dama sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa.

A farkon wannan watan ƙasashe 143 daga cikin ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193, sun kaɗa ƙuri'ar amince da Falasɗinu ta shiga cikin MDD, wani abu da ƙasa mai zaman kanta ne kawai ke samun damar haka.

Isra'ila ta kaddamar da yakinta a Gaza a matsayin ramuwar gayya kan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 1,200 tare da yin garkuwa da sama da 250, bisa kididdigar Isra'ila. Hare-haren Isra'ila a yankin sun kashe Falasdinawa sama da 35,000, a cewar ma'aikatar lafiya ta Gaza.