Iran: An Kashe Mutane 10 Cikin Dare

Zanga-zanga a Iran

Jami'an Iran na kokarin tsayar da zanga-zangar da jama'a ke yi akan kin jinin gwamanti a dalilin hakan ne ma suka toshe shafikansu na sada zumunci akan cewa suna taimaka wa wajen yada labarai akan zanga-zangar.

Gidan talabijin din kasar Iran ya bayyana a yau litinin cewa an kashe mutane goma cikin dare a yayin da ake ci gaba da zanga zangar kin jinin gwamnati da ta somo kuma ta yadu a kasar tun satin da ya gabata. Rahoton bai bada karin bayani a game da yadda mutanen suka mutu ba.
A safiyar litinin ne kamfanin dillancin labarai na ILNA ya bayyana cewa wani dan majalisar Iran din ya ce an harbe mutane biyu har lahira a cikin dare a garin Izeh dake kudu maso yammacin kasar, amma bai san wanene ke da alhakin wannan harbin ba.
Tashin hankalin dai ya soma ne daga karamar zanga zanga da akayi a birnin Mashdad wanda shine na biyu mafi girma a kasar ta Iran, kuma babban sansanin 'yan adawar shugaban kasa Hassan Rouhani a ranar alhamis din da ta gabata, kafin daga bisani ya yadu a sauran sassan kasar.
Gwamnatin shugaba Trump tace ta damu kwarai akan yadda Tehran ta hana Mutanen kasar Iran amfani da shafukan sada zumunci a kokarin ta na dakile zanga zangar.
Kasar Iran ta toshe hanyar tura sakonni ta Telegram, da dandalin watsa hotuna wato Instagram a ranar Lahadi, inda kafofin yada labarai na kasar suka ce anyi hakan ne domin a tabbatar da zaman lafiya domin 'yan kasar na amfani da shafukan su aika sakonnin zanga zangar. Wannan ita ce zanga-zanga mafi muni da aka taba yi ma shugabannin addini dake jan ragamar mulkin kasar tun shekarar 2009, a lokacin da aka nuna tunzurin rashin amincewa dasakamakon zaben shugaban kasa.