Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iran, Hassan Ruhani, Ya Kare Damar Iraniyawa Ta Yin Zanga-zanga


Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran
Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran

A wani al'amari na ba-zata, Shugaban kasar Iran Hassan Ruhani ya amsa cewa mutanen kasar na da izinin bayyana bacin ransa game da manufofin gwamnatin kasar ta hanyar zanga-zanga. Kalaman na Ruhani, da ake ganin wata hanya ce ta rarrashi da kuma iya tattalin hankalin wanda ake mulka idan ya fusata, ya yi ne a jawabinsa ga Majalisar Ministocinsa.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce mutanen kasarsa na da damar yin zanga-zanga da kuma sukar gwamnatin kasar; a martaninsa na farko game da zanga-zangar kyamar gwamnati da ake yi a fadin kasar, wadda ta shiga rana ta hudu jiya.

Gidan Talabijin na gwamnatin Iran ya ce Rouhani ya yi wannan kalamin faranta rai game da zanga-zangar ne a jawabinsa ga Majlisar Ministocinsa jiya Lahadi.

Zanga-zangar nuna kyamar gwamnatin, wadda ba a taba yin mai girmanta ba tun bayan zanga-zangar 2009 da aka yi game da sake zaben tsohon Shugaba Mahmoud Ahmadinejad, ta cigaba da aukuwa zuwa jiya Lahadi, ta yadda daruruwan mutane su ka yi ta shiga gangamin da ake yi bisa kan titunan fadin kasar, kamar yadda aka yi ta gani a faya-fayen bidiyon da mazauna unguwannin su ka yi ta tura ma Sashin Harshen Fasha na Muryar Amurka.
Daya daga cikin faya-fayen bidiyon da aka Tura ma Sashin Fasha na Muryar Amurka na nuna yadda wasu masu zanga-zanga ke kifar da wata motar ‘yan sanda a titin Valiasr da ke yankin tsakiyar birnin Tehran.

Wasu faya-fayen bidiyon kuma na nuna wasu mutane na daga murya sun a cewa “Allah ya ruguza mai shugabancin kama-karya” a birnin Urmia da ke lardin Azerbaijan na Yamma, a ke arewa maso yammacin Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG