Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Ta Barke Da Murnar Shiga Sabuwar Shekara


 Burj Khalifa, gini mafi tsawo a duniya da ke Dubai, ya haskaka wutar nuna murnar shiga sabuwar shekara.
Burj Khalifa, gini mafi tsawo a duniya da ke Dubai, ya haskaka wutar nuna murnar shiga sabuwar shekara.

Kamar yadda aka saba, kasashen duniya sun yi shagulgulan shiga sabuwar shekara ta 2018. Kamar kowace shekarar, wannan karon ma wasan hasken wuta ne ya rinjayi duk sauran shagulgulan shiga sabuwar shekara. Ga dukkan alamu dai an yi bukukuwan cikin kwanciyar hankali da lumana.

Jiya Lahadi mutanen Birnin New York, kamar sauran manyan biranen kasashen duniya, sun jure masifar sanyi mai ratsa jiki wajen tarbon sabuwar shekara. Haka su ma mazauna kasashen da ke yankin Gabashin Asiya da masu kai ziyara, sun marabci shekara ta 2018 da wasan hasken wuta da kuma shagugula.

Dubban mutane sun taru a gabar ruwa ta Victoria Harbor da ke Hong Kong don kallon wasan hasken wuta mai tafiya da kade-kade da raye-raye na tsawon minti 10, wanda ya hada da abin da aka yi lakabi da “taurari masu gudu” da aka harbo su daga rufin gine-gine.

A Jakarta babban birnin Indonesiya, rukunonin amarya da ango har sama da 400 ne aka masu auren bai daya, wanda hukuma ke daukar nauyi kowace shekara.

New Zealand, Australia da sauran kewayen yankin tsibiran Pacific dai na daya daga cikin wuraren da su ka fara shiga shera ta 2018.

Mutane kusan miliyan 1.5 ne su ka taru don kallon wasan hasken wuta mai kalar bakan gizo a sananniyar gadar nan ta gabar ruwa da ke birnin Sydney da kuma gidan shagulgula a yayin da kasar ke bukin halatta auren jinsi da aka yi.

A Amurka dai, jami’ai a Birnin New York sun bayar da sanarwar cewa za su yi amfani da tsarin bincike mai matakai biyu, da girke sojoji a saman gine-gine da katse wasu hanyoyi da kuma amfani da wasu karnuka na musamman don kare dandalin Time Square, yayin da mutane kimanin miliyan biyu su ka taru don kallon jefa wani kallon da akan yi shekara-shekara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG