‘Yan sanda a Iran sun ce za su fara amfani da fasahar zamani a wuraren da jama’a ke kai-komo don ganowa tare da hukunta matan da ke karya dokar saka hijabi a kasar.
Wata sanarwa da hukumomin Iran suka fitar a ranar Asabar ta ce, “za a fara amfani da na’urorin daukan hoto ko kyamara a wuraren da jama’a suke, domin gano masu bijirewa dokar.”
Sanarwar ta kara da cewa, “za a rika aikawa masu take dokar shaida da kuma sako na gargadi kan yiwuwar a dauki matakin shari’a akansu idan suka sake take dokar.”
Adadin matan da ke take dokar sanya hijabi a Iran na ci gaba da karuwa a ‘yan kwanakin nan, tun bayan jerin zanga-zanga da aka yi ta yi a lokacin mutuwar wata Bakurdiya ‘yar shekara 22 mai suna Mahsi Amini, wacce aka zarga da keta dokar.
Amini ta rasu ne a hannun ‘yan sandan Hisba a lokacin da ake tsare da ita bisa tuhumar karya dokar saka hijaba