Iran Ta Musanta Taimakawa 'Yan Tawayen Yemen

Minista Mohammad Javad Zarif

Iran ta ce bata yadda da zargin da ake mata ba na taimakawa 'yan tawayen Yemen a wajen kai hari kan Saudiyya, a saboda hakane ta ce zata binciki lamarin.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif, ya fadawa kafar yada labaran kasar yau Laraba cewa Iran zata binciki zargi mara tushe da Amurka, ta yi mata, na cewa ‘yan tawayen Yemen sun yi amfani da makaman da Iran ta basu don kai hari kan kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Islamic Republic News Agency, mallakar gwamnatin kasar ya ambaci Zarif na cewa take-taken Amurka, na tsokana ne, kuma Amurka na kokari ne ta boye goyon bayan ta akan kawanyar da aka yiwa bayin Allah ‘yan Yemen, shi ya sa bullo da wadannan zarge-zargen.

Iran ta taimakawa ‘yan tawayen Houthi, da suka kwace babban birnin Yemen, a shekarar 2014, amma ta musanta zargin cewa ita ta basu makamai. Amurka kuma na goyon bayan hadakar kasashen da Saudiyya ke jagoranta dake fafatawa da ‘yan Houthi, kusan shekaru 3 kenan don taimakawa shugaba Abdu Rabu Masour Hadi, wanda kasashen duniya suka amince da shi a matsayin shugaban kasar.