Zauren Majalosar Dinkin Duniya na shirin yin wani zama na gaggawa gobe Alhamis don gabatar da kudurin kin amincewa da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na amincewa birnin kudus ne babban birnin Isra’ila.
Jakadan Palasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Masour ne ya bukaci a yi taron ya kuma ce yana fata za a sami kwakkwaran goyon baya akan kudurin.
Kasar Masar ta gabatar da wani daftarin kuduri a gaban kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin Duniyar akan matakin na gwamnatin Amurka, shekaranjiya litinin, amma Amurka, ta yi amfani da ikonta na hawa kujerar na ki don dakile kudurin yayinda mambobin kwamiti 14 suka amince da shi.
Kuri’ar da zauren Majalisar zai kada akan kudurin da zai yi kama da wanda Masar ta gabatar, amma ba zai yi karfi ba a matsayin matakin kwamitin sulhu, babu tilas wajen bin kudurorin zauren majalisar, amma duk da haka za su iya sauya akalar siyasa.
Jakadiyar Amurka, a majalisar Nikki Haley ta yi kashedi gabanin kada kuri’ar akan cewa zata sa ido akan yadda wasu zasu kada kuri’a kuma zata gayawa shugaba Donald Trump, abinda ya faru.
Facebook Forum