Iran Ta Kai Karar Amurka a Gaban Kotun Duniya

Shugaban Iran Hassan Rouhani

Iran ta shigar da kara akan Amurka a gaban kotun duniya, kan umurnin da Shugaba Trump ya bayar, na a sake maido da takunkuman da aka dage mata, a karkashin shirin matsayar nukiliyan da aka cimma a shekarar 2015.
Wata sanarwa da kotun ta fitar a jiya Talata, ta nuna cewa, Iran na neman kotun ta ba Amurka umurnin ta dage takunkuman.


A cewar Iran, matakin na Amurka ya sabawa wata yarjejeniya da aka kulla a shekarar alif-dari-tara-da-hamsin-da-biyar a zamanin Sarkin Iran ko kuma Sha of Iran, a turance.


“Iran ta himmatu wajen bin doka da oda duk da irin matakin da Amurka ta dauka da ya sabawa tsarin diplomasiyya da dokokin da suka rataya a wuyanta.” Inji Ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Javad Zarif, a wani sakon Twitter da ya wallafa.


Sai dai wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, karar da Iran din ta shigar, ba ta da hujjar da za a iya sauraren ta.


A wani labari na daban kuma, kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta yi bikin cika shekaru 20 a wannan mako, karkashin wata yarjejeniya da ta kafa kotun, inda hankula suka fi karkata kan ingancin kotun yayin da take ci gaba da bunkasa.


An dai amince da dokar data kafa wannan kotu mai hedkwata a Hague ne a babban birnin Italiya, a ranar 17 ga watan Yulin shekarar alif-dari-tara-da-casa’in-da-takwas.


A yau, kotun na da mambobin kasashe 123 da suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniya.