Iran Ta Dauki Matakin Dakile Amfani Da Hanyar Sadarwa A Shirya Zanga Zanga

Zanga Zanga a Iran

Shugabannin kasar Iran sun koma kan hanyar da ta taimakawa masu bore suka iya hada kan masu zanga zangar nuna kin jinin gwamnati da aka gudanar na sama da mako guda kafin gwamnati ta shawo kansu, da nufin dakile sake aukuwar lamarin

Wani babban jami'in gwamnatin Iran ya yi kira a cikin makon nan ga hukumomi dake kula da harkokin tsarin hanyar sadarwar internet, su kara kula, domin kare sake aukuwar irin wannan boren.

Yayin wani taron koli kan fasaha a Tehran babban birnin kasar Iran, inda manyan jami'ai suka taru domin tattaunawa kan kalubalar kimiyya da kasar ke fuskanta, shugaban hukumar tsaron farar kaya Janar Gholamreza Jalali ya bayyana damuwa kan yiwuwar amfani da hanyoyin sadarwa wajen gudanar da wani bore.

A watan Disamba shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, dubun dubatan Iraniyawa suka shiga tituna suna zanga zanga, suna bayyana adawa da tsare tsaren gwamnati kan harkokin tattalin arziki da gazawar gwamnati ta samar da damar tattalin arziki ga 'yan kasa. Yayinda masu zanga zangar suna kuma neman karin 'yanci.