Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Tace An Kawo Karshen Zanga-zangar Da Akeyi Cikin Kasar


Masu Zanga Zanga Akan Tituna
Masu Zanga Zanga Akan Tituna

Kasar Iran tace ta shawo matsalar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki anay a cikkin kasar.Mahukuntar kasar suka ce zasu gudanar da taro domin gano dalilin wannan bore take da hana aukuwar haka nan gaba.

Jamian tsaro na musammam da ake ce ma Revolutionary Guard a turance na kasar Iran su,da sauran jamiaan tsaro sun samu nasarar murkushe zanga-zangar da aka jima ana yi a cikin kasar.

Jamian kaar sunce makiyan kasar,na kasar waje ne suka haddasa shi.

A cikin wata sanarwan da Gungun jamiaan tsaron suka fitar, sunce anyi nasarar ne ta yunkurin hadin gwiwar da jamiaan tsaro daban-daban na kasar sukayi.

Suka ce ba kowa ne ya haddasa wannan ba illa Amurka,Birtaniya, Iszaela, da kuma gidan saurautar Saudi Arabia, sai kuma haramtacciyar kungiyar Majahedin.

Yanzu haka dai majilisar zartaswan kasar ta Iran tana gudanar da taro na musammam a yau lahadi,domin duba zanga-zangar da aka fara tun daga ranar 28 na watan jiya wanda yaci gaba har kawo yanzu da suka sha karfin sa.

Kanfanin dillacin labaran kasar ta Iran ISNA tace Ministan cikin cikin gidan yace Cikin wadanda zasu halarci wannan taron na majilisar, harda shugabannin hukumar leken asiri,da sauran jamiaan hukumomin tsaro.

Kuma babban abinda taron zai mayar da hankali akai shine gano musabbabin wannan zanga-zanga tare da duba abinda doka tace game da wadanda aka tsare sakamakon wannan zanga-zangar.

Wasu ‘yan majilisar dokokin kasar ne suka nemi a gudanar da taron, haka kuma sun bukaci a samar da taimakon lauyoyi ga wadanda aka kame sakamakon zanga-zangar.

Sai dai sunyi ALLAH waddarai da kasashen waje da suka ce sune suka haddasa wa kasar tasu wannan zanga-zangar musammam ma Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG