Iran: Obama Ya Yi wa Amurkawa Karya - Trump

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyar Republican, Donald Trump

‘Yan jami’iyar Republican ta nan Amurka suna sukar lamirin gwamnatin shugaba Obama akan wani labari da ya fito Alhamis cewa Amurka ta kashe dala miliyon 400 wurin karbo wasu Amurkawa ‘yan fursuna dake zaman gidan yari a Tehran.

Kakakin Majalisa Paul Ryan ne ya fitar da wannan sanarwa yana cewa shugaba Obama da gwamnatinsa suna yaudaransu tun watan Janairu kuma dole ne shugaban ya yiwa Amurkawa cikakken lissafi akan wannan mataki nasa.

Dan takarar shugaban kasa na Republican Donald Trump ya kira shugaba Obama a matsayin makaryaci saboda ya musanta biyan fansar karbo Amurkawan tun farko.

Shugaban kwamitin harkokin waje a majalisa kuma dan jam’iyar Republican Ed Royce ya ce biyan wannan kudin fansar ya jefa rayuwar dimbin Amurkawa cikin hadari. Kuma sun karawa Iran karfi.

Ya ce a gaskiya suna kara basu karfin gwiwa da su ci gaba da yin garkuwa da mutanensu.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka sau tari tana musunta biyan wannan fansar.

Tsare tsaren gwamnatin Amurka ya haramta biyan kudin fansa don kada a ba da damar ci gaba da yin garkuwa da Amurkawa.

Gwamnatin ta Obama dai ta ce kudaden na Iran ne wanda ta yi niyyar sayen makamai tun a shekarun 1970.