Hukumar Majalisar Dinkin Duniya MDD mai sa ido kan nukiliya (IAEA), ta fadi jiya Alhamis cewa Iran na mutunta sharuddan da yarjajjeniyar kasa da kasa ta 2015 ta gindaya ma ta game da shirnta na nukiliya, wanda shi ne bayanin sifetocin bincike na farko tun bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya janye Amurka daga yarjajjeniyar
Hukumar ta IAEA ta ce Iran ta tsaya daidai yadda aka bukaci ta yi game da batun ingnta sinadarin Uranium, da adadin sinadarin Uranium din da ta iza da kuma sauran sharudda
To amma hukumar ta MDD ta ja-kunnen Iran saboda takaita wuraren da za a iya dubawa yayin bincike.
Wannan bayanin na MDD na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta kakaba sabbin takunkumi kan Iran a wani yinkuri na matsa lamba ma Janhuriyar Ta Musulunci ta zo teburin tattauwa saboda a sake lale game da yarjejjeniyar nukiliya, ta takaita gwaje-gwajen makamai masu linzami ta kuma kawo karshen girke sojojinta ko sa su kutse a yankin Gabas Ta Tsakiya.