A safiyar yau Juma’a ne sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya hadu da ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif da wasu jami’an kungiyar tarayyar Turai a wani Otel inda suke gudanarda wannan tattaunawar tasu.
Alokacin da Zarif yake magana a Otel din yace, an samu cigaba cikin tattaunawar da ake. Amma bayan da wani ‘dan jarida ya tambayeshi ko zai zauna hutun ‘karshen mako a babban birnin na Australia? Ya kuma ce “a kwai alamun haka.”
Ya cigaba da cewa, “bamu dawani kayyadaden wa’adi, kuma ina son mu samu yarjejeniya mai kyau.”
Sai dai kuma a lokacin da tattaunawar ta shiga mako na biyu, akwai alamar kosawa a wurin mahalartan, abinda ya kai a daren jiya Alhamis ne Zarif ya fito yana sukar lamirin wasu kasashen duniya da yace suna nuna canji inda suke ‘karawa kansu bukatun da bana dole ba.
Sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry ya bayyana jiya Alhamis cewa, idan ba a cimma matsaya a tattaunawar da ake yi kan ayyukan nukiliyan Iran ba, a shirye masu tattaunawar Amurka suke su kawo karshen zaman.
Kerry ya shaidawa manema labarai cewa, ba zasu yi gaggawa ba, kuma babu wanda zai matsa musu lambar suyi gaggawar.” Amma duk da haka yace an sami ci gaba ainun da zai kai ga cimma matsaya mai ma’ana, sai dai abinda ake damuwa a kai shine ingancin yarjejeniyar.