Manufar samamen mai taken “Operation Jackall III”, wanda ke gudana tun daga ranar 10 ga watan Afrilun da ya gabata zuwa 21 ga watan Yulin da muke ciki, shine yakar matsalar damfarar kudade ta yanar gizo da kungiyoyin dake gudanar da ita a kasashen shiyar yammacin Afrika, a cewar sanarwar da Interpol ta fitar.
Daraktan sashen cibiyar yaki da laifuffukan da suka shafi kudi da almundahana ta Interpol, Isaac Ogini, yace mizanin damfarar kudaden dake gudana a yammacin Afrika ya kasance abin tashin hankali kuma har yanzu ba’a kai ga shawo kansa ba.
“Sakamakon samamen ya sake bayyana bukatar samun hadin kai tsakanin hukumomin tsaron kasa da kasa domin yakar gungun kungiyoyin dake wannan ta’annati masu yawan gaske.”
A cewar Interpol, da ya daga cikin kungiyoyin da ake sawa idanu ita ce “Balck Axe”, guda daga cikin kungiyoyin batagarin da ta yi kwarin suna a shiyar yammacin Afrika.
Ayyukan Black Axe sun hada da damfara ta yanar gizo da safarar bil adama da fasa kwabri kuma ta na da hannu a tashe-tashen hankula a nahiyar Afrika dama duniya baki daya.
Black Axe na amfani da dillalan safarar kudade wajen bude asusun ajiyar banki a fadin duniya kuma ana gudanar da bincike akanta a fiye da kasashe 40 akan laifuffukan dake da nasaba da halasta kudaden haram, a cewar rundunar ‘yan sandan Interpol.
Wadanda ake zargin sun hada da ‘yan kasashen Argentina da Colombia da Najeriya da Venezuela.
A kasar Argentina, biyo bayan bincike na tsawon shekaru 5, ‘yan sanda sun yi dirar mikiya akan Black Axe tare da kwato kudaden jabu har dala miliyan 1 da dubu 200 sannan suka kama mutane 72 da rufe akalla asusun ajiyar banki 100.
-AP