WASHINGTON, D.C —
An rataye wasu mutane su 4 har lahira a yau Juma’a a kasar Indiya, bayan da aka yanke musu hukunci akan laifin fyade da kuma kashe wata daliba ‘yar shekara 23 da haihuwa a birnin New Delhi.
Wannan shari’ar dai ta maida hankali ne akan cin zarafin mata a India. An yi ta zanga-zangar neman karin kariya ga mata bayan faruwar mummunan fyaden da aka yi wa yarinyar a shekara ta 2012 a cikin wata motar bas.
Yanzu haka dai gwamnati ta saka jami’an tsaro da na’urorin daukar hoton bidiyo a motocin safa. To sai dai mata a kasar na cewa tabarbarewar tarbiyya ita ce babbar matsalar.