Wasu tsoffin makusantan shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan su biyu, sun kafa sabbin jam'iyyun siyasa, matakin da ake ganin zai iya yin barazana ga mulkinsa.
Jam'iyyun biyu na kokari ne su dabbaka abin da suke kira samar da sahihiyar demokradiyya a kasar, inda aka sakawa daya daga cikin jam'iyyun suna Deva, wato makari.
Shugaban wannan jam'iyya Ali Babacan, na daya daga cikin tsoffin na hannun daman shugaba Erdogan, kuma jam'iyyarsa ta kuduri aniyyar ganin ta kawo karshen mulkin Erdogan.
Baya ga shi, akwai tsohon firai minista Ahmet Davutoglu, wanda shi ma zai kalubalanci Erdogan a zaben da za a yi karkashin jam'iyyarsa ta Gelecek, wacce take ta tallata yadda tsohon firai ministan ya kafa tarihi, a matsayin wanda ba a taba samun shi da laifin cin hanci da rashawa ba, yayin da ake zargin jam'iyyar Erdogan ta AK da hannun dumu-dumu da laifukan da suka jibinci rashawa.
Facebook Forum