Inda Wata Kyakkywar Budurwa Ce Da Yanzu Wani Ya Kaita Asibiti: Emeka Ike

Tsohon jarumin Nollywood mai suna Emeka Ike, ya bayyana yawancin ‘yan Najeriya basu, kokuma sun ki su taimakawa jamruminnan Prince James Uche, dake fama da rashin lafiya tunda shi ba wata kyakkyawar budrwa bace.

Idan ba’a manta ba jarumin ya kwana biyu yana fama da rashin lafiya mai nasaba da ciwon koda, kuma yana bukatar taimakon gaggawa domin a yi masa dashen koda a kasar India.

Shekaru takwas kenen da Jarumin ke fama da hawan jini, da ciwon suga da kuma ciwon koda, na kwane ne a asibitin Godspower dake C-Close, a jihar Legas, harma ance idanunsa sun daina gani.

Rahotanni sun bayyana cewa sau tari ana korarsa daga asibitin a sakamakon rashin biyan kudin jiyya, amma rahotanni sun bayyana cewa ya sake komawa asibitin bayan wasu masu hannu da shuni sun tallafa masa da kudi.

Mujallar Daily Post ta wallafa cewa Jarumin nan kuma shugaban kungiyar masu fina finai wadda ake kira Actors Guild Of Nigeria, y ace abin bakin ciki ne yadda dan Najeriya guda zai iya daukar dawainiyar kai jarumin asibiti amma kowa ya juya masa baya.

Daga karshe ya bayyana cewa da ace wata kyakkyawar yariya ce take fama da rashin lafiya haka da yanzu wani ya dauki dawainiyar kaita asibiti amma da shike tsoho ne shiyasa jama’a sukia yi kunnen uwar shegu da lamarin.