Ina Makomar 'Yan Mata Masu Shaye Shaye A Rayuwar Aure? Ra'ayoyin Samari Mashaya

Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, a wannan karon, shirin samartaka ya sami zantawa ne da wasu samari masu shan abubuwa dangin su totolin da sauran su, koda shike shan kayan maye ba dabi’ar kirki bace dan haka ne muka tambaye su, shin ko zasu iya auren mata masu aikata irin wannan dabi’a? da kuma irin kalubalen da suke fuskanta wajan neman aure.

Akasarin wadanda muka yi hirar da su, sun bayyana mana cewa batun kalubale bai taso ba domin kuwa suna da abokai ‘yan mata da dama da ke aikata irin wannan dabi’a ta shaye shaye, dan haka wannan a cewar su ba matsala bace.

Da muka so muji ra’ayoyin su dangane da irin yanayin da suke samun kansu a yayin da suke cikin maye, samarin sun bayyana mana cewar sukan ji tamkar idanun su a taitsaye suke domin babau maganar kunya, kuma sun kara da cewa akwai ‘yan mata da dama da har yanzu basu san samartin sun a shaye shaye ba.

A karshen tattaunawar mun tambaye su batun aure, tunda sukan hadu da ‘yan matan har su sha tare, dan haka mai zai hana su aure su? Matasan baki daya suka nuna nuna cewar atafau baza su yarda da wannan shawar ba domin kamar yadda wani daga cikin su y ace, idan ya auri mai shaye shaye kokuma abokiyar da suke shaye shayen tare babu wanda zai ba wani shawara Kenan,

Daga karshe sun bayyana cewar da zarar lokacin da zasu yi aure ya karato zasu garzaya wurin magabatan su domin su sama masu ma’aurata na kwarai.

Saurari cikakkiyar hirar.