Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana cewa yana da cikakken ikon yiwa kansa afuwa dangane da ake yi, daga nan kuma ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa binciken da gwamnatin tarayya ke yi akan alaka tsakanin wadanda suka yi mashi yakin neman zabe a shekarar 2016 da Rasha kwata-kwata baya cikin tsarin mulki.
Tun bayan da ya hau kujerar shugaban kasa kwanaki 500 da suka gabata, shugaba Trump ya sha yin watsi da ka’idodin da aka gindaya, ya kuma kalubalanci iyakokin ikon da aka san shugaban kasa da su. Amma maganganun da yayi na baya-baya, musamman akan fidda kansa, abin mamaki ne sosai kuma abin muhawara ne a fannin shari’a.
Susan Low Block, wata farfesa a Jami'ar Georgetown ta nan Amurka ta ce, "Ina tunanin zai yi wuya shugaba ya zare kansa. Ina gani kotu ba zata amince ba. Amma kuma ina gani idan har shugaba zai iya fidda kansa, yawancin ‘yan majalissa zasu tumbuke shi."
Ko da yake lauyoyin Trump, na kokarin duba batun ta bangaren shari’a akan cewa ikon shugaban kasa na da yawa sosai, yana da ikon ya kawo karshen bincike na musamman da ake yi wa wadanda suka yi mashi yakin neman zabe ko kuma ya zare kansa abinda ya fi kama da mulkin sarkin gargajiya amma ba zababben shugaba ba.
Lauyoyin Trump, a wata doguwar wasika da suka rubutawa shugaban kwamitin binciken na musamman a watan Janairu da ta fito fili kwanan nan, sun ce ba za a iya tursasawa shugaban kasar ya bada bahasi ta wajen amfani da ikon sammace ba, suka kuma ce bai keta doka ba ta wajen korar darektan hukumar leken asiri dake jagorantar binciken katsalandan da ake zargin Rasha tayi, sabili da shugaban kasar yana da ikon dakatar da binciken.