Ina Aka Kwana Dangane Da Cin Zarafin Wasu Yara A Jahar Kano?

A rahoton mu na makonin da suka gabata, mun bayyana maku cewa alamu sun nuna cewa gwamnatin jahar kano ta jingine rahoton kwamitin da ta kafa domin bincikar zargin lalata yara a makarantar sakandire ta Hassan Gwarzo, a maimakon haka gwamnati ta dauki matakin ganawa da iyayen yaran kai tsaye kamar yadda guda daga cikn su ya bayyana mana.

Malamin ya ce "za'a iya cewa an neme mu ba'a neme mu ba, tunda mu abin da muka yi tsammani shine mu da muke da korafe korafe akan wannan ciwo da aka jawo mana, za'a kiramu a dunkule baki daya domin tattaunawa akan dukan batutuwan tunda dai akwai duk wasu shaidu da hujjoji da suka tabbatar da aukuwar lamarin. Amma sai muka ga ba tsarin da aka dauko ba kenan".

Malamin ya cigaba da cewa ance za'a neme mu daya bayan daya amma haryanzu shiru kake ji. duk acikin wadanda aka aikataw wannan mummunar aika aika, mutum guda kadai aka nema, kuma koda aka neme shi hakuri kadai aka bashi.

Sai dai kwamishinan yada labarai na Kano ya bayyana wa wakilin muryar Amurka Ibrahim Kwari cewar a larabar jiya ne majalisar zartarwa ta jahar kano zata ta tattauna tare da fitar da matsaya game da batun.

Saurari cikakken rahoton a nan...Dandalinvoa.com