Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Kalilan Ne Suka san Abunda Dumamar Yanayi Ke Nufi


Wani bincike da aka gudanar kan dumamar yanayi a Najeriya, na nuni da cewa mutane kalilan ne suka san abunda dumamar yanayi ke nufi.

Wani karamin manomi Malam Babangida Sidi Akwanga, ya shi kam bai san da wannan batu ba da aka tambayeshi batun zafi sai ya ce zafi kam akwai shi domin ko akan dabbobi ma zaka gane akwai alamar zafi domin yanzu ga koramu sun bushe tun lokaci bayyi ba kuma da har damuna yazo ana ganin shi da ruwa wani lokaci sai anyi tafiyar kusa kilo mita 20, zuwa 30 kafin su samu ruwan da za’a sub a dabbobi, yanayin wuri ya canja baki daya wurare sun bushe da duk fadamar shinkafa ne ruwa har bakin gidaje yanzu kasha wurin baki daya ya bushe.

Kamar dai alumomin dake karkara da alamun wasu dake ma biranai basu san da wannan matsallar ba. Wannan mako na zuwa ne yayin da ake haramar taron koli da za’a gudanar kan matakan kare duniya da matsalar dumamar yanayi.

Dr. Amoga Kaftin Namala, Malami a jami’ar Kimiya da Fasaha ta Moddibo Adam, dake Yola, ya ce idan anason a yaba talakawa da jin radadin matsalar sauyi yanayi to yakamata a inganta kiwon lafiyarsu tare da daukar matakan karesu daga matsalar ambaliyan ruwa da kuma lalacewar amfanin Gona, haka nan kuma masanin ya ce dole ne a sa ido game da yadda ake fitar da gurbatatcen iska da jama’a ke shaka.

XS
SM
MD
LG